Yan matan Dapchi: Shugaba Buhari ya isa garin Damaturu don ganawa da iyayen yan matan
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa babban birnin jihar Yobe, Damaturu a cigaba da ziyarar dayake kaiwa jihohin da matsalolin tsaro suka fi ta’azzara kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Buhari ya fara sauka ne da jirgin shugaban kasa a garin Maiduguri na jihar Borno, daga nan ya tashi da misalin karfe 12 na rana cikin jirgi mai saukan angulu tare da gwamnan Borno, Kashim Shettima zuwa Damaturu.
KU KARANTA: Hare haren yan bindiga a Filato: El-Rufai ya tsaurara matakan tsaro a iyakar Kaduna da Filato
Gwamnan jihar Yobe Ibrahim Gaidam ne ya tarbi shugaba Buhari da tawagarsa a filin wasa na Damaturu, inda Buharin ya sauka, daga nan kuma suka wuce fadar gwamnatin jihar, yayin da suke kan hanyarsu Buhari yayi ta karbar gaisuwa daga jama’a da suka yi layi a kan titunan garin.
Shugaba Buhari ya shirya wannan ziyara ne da nufin ganawa da iyayen dalibai yan matan sakandarin kimiyya dake garin Dapchi, su 110 da yan ta’addan Boko Haram suka sace kimanin sati uku da suka gabata.
Hakazalika ana sa ran shugaba Buhari zai tattauna da sarakunan gargajiyar jihar, shuwagabannin siyasa da kuma masu ruwa da tsaki a jihar a wani babban taron jin ra’ayin jama’a, kamar dai yadda fadar shugaban kasa ta tabbatar da hakan.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng