Yanzu-Yanzu: Hukumar shirya jarabawar WASSCE ta saki sakamokon 2018

Yanzu-Yanzu: Hukumar shirya jarabawar WASSCE ta saki sakamokon 2018

Hukumar nan dake da alhakin shirya jarabawar kammala makarantar Sakandare ta yammacin Afrika watau West African Examination Council, WAEC a jiya ta sanar da fara fitar da sakamakon jarabawar da ta gudanar ga dalibai a cikin farkon shekarar nan ta 2018.

Da yake sanar da hakan a babbar hedikwatar hukumar dake garin Legas, shugaban hukumar Mr. Isaac Adenipekun ya bayyana cewa cikin dalibai 11,307 da suka zauna jarabawar, akalla mutane 1,937 ne kacal suka samu nasarar lashe darussa 5 zuwa sama da suka hada da Turanci da kuma Lissafi.

Yanzu-Yanzu: Hukumar shirya jarabawar WASSCE ta saki sakamokon 2018
Yanzu-Yanzu: Hukumar shirya jarabawar WASSCE ta saki sakamokon 2018

KU KARANTA: Yadda za muyi zaben fitar da gwani - PDP

Wannan acewar sa babbar rashin nasarar ce idan aka yi la'akari da cewa hakan na nuni ne da cewa kaso 83 cikin dari na daliban duk sun fadi jarabawar.

A wani labarin kuma, Jami'an tsaron farar hula na gwamnatin tarayya Nigerian Security and Civil Defence Corps, NSCDC shiyyar garin Abuja, babban birnin tarayya a jiya sun gabatar da wasu mutane biyu ga manema labarai bisa laifin aikata satar ansa yayin gudanar da jarabawar share fagen shiga jami'a watau Unified Tertiary Matriculation Examination (UTME).

Kamar yadda muka samu kuma, cikin wadanda aka gurfanar din sun hada da wata mace wadda aka zarga da boye wayar salula a cikin dan tofin ta wadda kuma take anfani da ita wajen satar ansa a yayin jarabawar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng