Zan tsaya takarar shugaban kasa muddin Kwankwaso ya ja da baya – Inji Buba Galadima

Zan tsaya takarar shugaban kasa muddin Kwankwaso ya ja da baya – Inji Buba Galadima

Jigo a cikin jam’iyyar APC, Alhaji Buba Galadima ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2019 don karawa tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari, inji rahoton Daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Galadima ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da yayi tare da gidan rediyon muryar Amurka, a cikin shirin tsaka mai wuya a ranar Talata 13 ga watan Maris.

KU KARANTA: Babban dalilin da yasa gwamnan jigawa ya sa Yansanda su kamo masa wani ɗan jarida

A cikin tattunawar, Galadima yace muddin Sanatan Kano ta tsakiya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ja da baya, ya fasa tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2019, tabbas shi zai tsaya don fafatawa da shuga Buhari.

Zan tsaya takarar shugaban kasa muddin Kwankwaso ya ja da baya – Inji Buba Galadima
Buba Galadima

“Bari in fada ma Duniya zan goyi bayan Kwankwaso idan ya yanke shawarar tsayawa takara a shekarar 2019, saboda na gamsu da cewa Kwankwaso zai karkata akalar Najeriya zuwa cigaba, tare da magance matsalolin jam’iyyar APC.

“Ba zamu yarda da dauki daura a jam’iyyar APC ba, zamu tabbatar da an gudanar da zabukan cikin gida a cikin jam’iyyar, kuma Kwankwaso nake so, amma idan ya ja da baya, zan tsaya takara don in fafata da Buhari.” Inji shi.

Baya da haka, Buba ya soki Buhari, inda ya daura masa laifin dukkanin rikita rikitan dake wakana a cikin gidan jam’iyyar APC; “A yan kwanakin nan, Buhari ya kai ziyara jihar Kano, Kaduna da wasu jihohi, amma bai kira shuwagabannin APC na don tattauna matsalolinsu.”

Sai dai daga karshe Buba yayi kidarsa yayi rawansa, inda yace shi fa ba wai yana sukan Buhari bane, ko kuma yana adawa da shi ba, “Ina fada masa gaskiya ne kawai don ya gyara matsalolinsa, tare da cika ma yan Najeriya alkawurran da ya daukan musu.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel