Ta tabbata ba Buhari ke mukin kasar nan ba - Matashin dan takarar shugaban kasa

Ta tabbata ba Buhari ke mukin kasar nan ba - Matashin dan takarar shugaban kasa

Wani matashi wanda yake da ra'ayin fitowa takarar shugaban kasa a zaben 2019 mai suna Adamu Garba II ya fito ya bayyana cewa yanzu dai kam ta tabbata cewa ba shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ba ke mulkar Najeriya.

Matashin dai ya bayyana hakan ne a yayin da yake maida martani a shafin sa na Tuwita mai adreshin @adamugarba game da kalaman shugaban da ya yi a jihar Benue inda yace yayi mamaki da aka gaya masa cewa shugaban 'yan sandan Najeriya yayi fatali da umurnin da ya bashi na komawa jihar Benue din.

Ta tabbata ba Buhari ke mukin kasar nan ba - Matashin dan takarar shugaban kasa
Ta tabbata ba Buhari ke mukin kasar nan ba - Matashin dan takarar shugaban kasa

KU KARANTA: Kannywood sun yi rashin babban jarumi

Legit.ng ta samu cewa sai dai Adamu Garba, wanda fitaccen dan kasuwa ne ya bayyana cewa wannan ko shakka babu yana nuni ne da cewa shugaban kasar ya gaza wajen bayar da sahihin shugabanci ga 'yan kasa.

Daga karshe ne kuma sai Adamu din ya roki 'yan kasa da su bashi dama domin shi a shirye yake da ya bayar da ta sa gudummuwar da kuma kwarewar sa.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a baya ma Gwamnan jihar Ekiti dake a yankin kudu maso yammacin kasar nan kuma sanannen mai adawa da shugaba Buhari ya sake nanata bukatar sa ga Buhari na yayi murabus daga mukamin sa bisa dalilan abun da ya kira rashin tabuka komai ga kasar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng