Kayan hadin bom: Gwamnatin tarayya ta zayyana yadda ta karya lagon 'yan Boko Haram
Gwamnatin tarayyar Najeriya a karkashin shugabancin shugaba Muhari ta bayyana yadda ta dauka tare kuma da cigaba da daukar wasu muhimman matakai don ganin ta dakile 'yan Boko Haram daga samun kayayyaki da sinadaran da suke anfani da su wajen hada boma-bomai.
Wannan dai na kunshe ne a cikin jawabin maraba da babban mai baiwa shugaban kasa shawara ta fuskar harkokin tsaro Babagana Monguno yayi yayin taron masu ruwa da tsaki a harkokin sinadarai.
KU KARANTA: Ali Modu Sheriff ya sha tambayoyi wurin EFCC
Legit.ng ta samu cewa Monguno, wanda ya samu wakilcin babban mataimakin sa Mista Yamin Ehinnomen Musa ya bayyana cewa ofishin su ya dauke wasu muhimman matakai ne a tsanake tare kuma da hada kai da sauran manyan ma'aikatun gwamnatin domin hana sinadaran zuwa hannun bata-gari.
A wani labarin kuma, Dan majalisar dattijan Najeriya daga jihar Nasarawa kuma shugaban kwamitin harkokin noma Sanata Abdullahi Adamu a jiya ya bayyana cewa shi fa ba bu wani kalar razanarwa daga abokan aikin sa da za ta sa ya dena goyon bayan shugaba Buhari.
Haka kuma Sanatan wanda ke zaman tsohon gwamnan jihar ta Nasarawa ya kuma bayyana cewa hakika abun takaici ne yadda yawacin 'yan majalisar jam'iyyar APC mai mulki suke munafuntar gwamnatin shugaba Buhari duk kuwa da zaman su a jam'iyya daya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng