Ban taba sanin Sfeto Janar na ‘yansanda ya koma jihar Nasarawa ba bayan na umarce shi ya koma jihar Benuwe - Buhari
- Buhari ya ce an cigba da kashe-kashe a jihar Benuwe ne saboda Sfeto Janar na ‘yansanda ya ki bin umarnin sa
- Shugaba Buhari ya gana da dattawan jihar Bneuwe a birnin Makurdi
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce bashi da masaniya akan adadin ranakun da Sfeto Janar na yansandan Najeriya, Ibrahim Idris ,yayi a jihar Benuwe bayan ya urmace shi ya koma jihar.
Shugaba Buhari, ya bayyana haka ne a ranar Litinin a lokacin da yake ganawa da dattawan jihar Benuwe a birnin Makurdi.
Buhari ya ce an cigaba kashe-kashe a jihar Benuwe ne saboda Sfeto Janar na ‘yansanda ya ki umarnin sa.
A ranar 9 ga watan Janairu ne, shugaba kasa, Muhammadu Buhari, ya umarci sfeto Janar na ‘yansanda ya koma jihar Benuwe da zama, saboda kawo karshen kashe-kashen da ake yi a jihar.
KU KARANTA : Bukin diyar Ganduje, tashin hankali ne ga musulunci da tarbiyyar ‘ya’yan mu – Sheikh Gumi
Bayan ya bi umarnin shugaban kasa ya koma jihar Benuwe daganan sai, IGP Ibrahim Idiris, ya arce zuwa jihar Nasarawa.
A lokacin da yake zantawa da Dattawan jihar Benuwe a birnin Markudi, shugaba Buhari ya ce bai taba sanin Sfeto Janar na ‘yansanda ya koma jihar Nasarawa ba bayan na umarce shi ya koma jihar Benuwe ba.
Buhari ya bayyana haka ne bayan gwamna Samuel Ortom, ya roki shi, ya shawarci, IGP Ibrahim Idris, ya daina shiga harkar siyasa da kuma nuna bangaranci a matsayin sa na shugaban 'yansandan Najeriya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng