A Najeriyar mu: Yadda wani saurayi mai shekaru 23 ya auri kanwarsa mai shekaru 16

A Najeriyar mu: Yadda wani saurayi mai shekaru 23 ya auri kanwarsa mai shekaru 16

Wani abu mai ban al’ajabin da ya faru a unguwar Ekwulobia dake cikin karamar hukumar Aguata na jihar Anmabra, inda wani matashi ya auri kanwarsa na cigaba da tayar da kura a tsakanin al’ummar garin.

Wannan lamari dai ya faru a tsakanin matashin mai suna Chiadikobi Ezeibekwe, dake koyarwa a makarantar sakandarin da garin Ekwulobia da kuma kanwarsa uwa daya uba daya da ba’a bayyana sunanta ba, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Tsoho ya ga Canji: Sai yancu na san ana mulkin Dimukradiyya - Inji wani Dattijon da ya samu aiki a Jigawa

Sai dai gidan talabijin na The Channels yayi tattaki har zuwa garin Ekwulobia, inda ya samu ganawa da iyayen yaron, Yayansa wanda ya daura auren, Sarkin garin, har ma da Angon da Amaryarsa.

A zantawarsa da majiyar Legit.ng, Angon yace wannan ba wani abu bane illa cika umarnin Ubangiji daya samu ta hanyar wahayi, don haka bai damu da surutan da ake ta yayatawa a kansu ba, ita ma Amaryar mai shekaru 16 ta rungumi auren a matsayin hanyar cika umarnin Ubangiji.

Angon ya kara da cewa: “Amfanin wannan aure shine ba za’a taba rabuwa ba, kaga babu maganar saki, kuma yana kara dankon zumunci, bana jin kunya, bana jin tsoron abinda wani zai iya min, Ubangiji ne kadai zai iya warware wannan aure.”

Sai dai matasan garin sun yi kona cocin yayan Angon, wanda shine kanwa uwar gami wajen daura auren Angon da kanwarsu, inda shima yace yana cika umarnin wahayin Ubangiji da kaninsa ya samu ne.

Amma da aka ji ta bakin sarkin garin, Gabriel Ezeukwu, yace ba zasu lamunci wannan barna da abin kunya a garinsu ba, don haka yace sun yi kokarin sallamarsu daga garin gaba daya, amma yace wannan al’adar dauri ce, don haka suna ta kokarin lalubo hanyar warware matsalar nan a yanzu.

A yanzu dai an dakatar da Ango da Amarya daga saduwa da juna har sai an lalubo hanyar warware wannan lamari, inda uwar ma’auratan tace a shirye suke su bi dukkanin matakan da suka dace da za’abi don shawon kan matsalar, amma yayanta ba zasu rabu ba, sai Ubangiji ya bada umarnin hakan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng