Hatsarin Mota: Wani direba da yayi tatul da ruwan barasa ya kashe mutane hudu a kofar shiga Lekki (Toll Gate)
- Wani direba mashayin giya ya kashe mutane hudu da raunana mutane 16 a jihar Legas
- Hukumar LASEMA ta shawarci direbobi su daina gudu akan manyan hanyoyi da kuma tuki a lokacin da suka sha ruwan barasa
Bala’i ya afkawa wa jihar Legas yayin da wani direban Bas mai suna, Gbeminiyi Odeniyi, ya buge wata motar dibar fasinja akan babban titin Lekki Epe dake kusa da kofar shiga dake Lekki(Toll gate).
Legit.ng ta samu rahoton cewa, mutane biyu sun mutu a take wajen, sai kuma biyu sun kara mutuwa a asibitin, Lagos Island General Hospital, dake unguwar Marina.
Fasinjoji 16 sun samu munanan rauni ta sanadiyar hastsarin.
KU KARANTA : Amfani 10 na ganyen Gwaiba ga lafiyar dan Adam
Legit.ng ta samu rahoton cewa kungiyar direbobin Bas na jihar Legas su fara gudanar da zanga-zanga akan hukumar kofar shiga dake Lekki (Toll Gate) sai suka dakatar bayan sun fahimci cewa direban bas dan uwan su ne ya janyo hatsarin, wanda ake zargi yayi tatul da ruwan barasa kafin ya fara tuki.
Shugaban kula da hanyoyin na jihar Legas LASEMA, Adeshina Tiamiyu, ya tabatar da aukuwan wannan lamari, inda ya shawarci direbob su rika tuki a hankali akan manyan tittunan jihar kuma sai daina tuki a lokacin da suka sha ruwan barasa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng