Shugaba Buhari ya jajantawa iyalan tsohon gwamnan jihar Adamawa Alhaji Saleh Michikah
- Buhari ya jajantawa iyalan tsohon gwamnan jihar Adamawa Alhaji Saleh Michikah
- Mutuwar Saleh Michika babban rashi ne ga al'ummar jihar Adamawa da Najeriya baki daya inji shugaba Buhari
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya mika sakon ta’aziyar sa ga gwamnati da dukannin al’ummar jihar Adamawa akan mutuwar tsohon gwamnan jihar, Alhaji Saleh Michikah da ya rasu a daren ranar Asabar.
Shugaba Buhari ya jajantawa iyalan mamacin akan babban rashin da suka yi.
Buhari ya kwatanta shi a matsayin Dattijo mai adalci wanda ya kawo wa jihar sa cigaba, kuma mutum ne mai kishin al’ummar sa.
KU KARANTA : Zaben 2019 : Za'a sake saida katin neman tallafi wa Buhari kuwa? – Ashafa Murnai
Shugaba Buhari yayi imani cewa ‘yan Najeriya za su yi kewan sa sosai saboda irin gundumawar da ya bada wajen cigaban kasar, mussaman shawarwarin sa na alheri da kuma yadda yake gudanar da harkokin rayuwar sa cikin sauki.
Shugaban kasa ya aika tawagar gwamnatin tarayya karkashin jagorancin sakataren gwamnati, Boss Mustapha, a madadin sa zuwa jihar Adamawa dan janjantawa iyalan maragayin da kuma mutanen jihar.
Babban hadimin shugaban Kasa a fannin watsa labaru, Femi Adesina ya bayyana haka a shafin sa na Facebook.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng