Dandalin Kannywood: Fitattun 'yan fim din Hausa sun caccaki sharholiyar bikin diyar Ganduje
Wasu fitattu a masana'antar shirya fina-finain Hausa da ake yi wa lakabi da Kannywood sun nuna bacin ran su kan rashin tsawatawar da malaman addinai da kuma hukumomi suka ki yi a kan hotunan diyar gwamnan jihar Kano Fatima da Idris dan gwamnan jihar Oyo.
Hotunan dai na shagalin bikin auren na ma'auratan sun yi ta jawo zafafafn muhawarori a kafafen sada zumunta kamar wutar daji, bayan an gan inda suka rungumi juna har hannun angon na ta ya kai ga kirjin ta.
KU KARANTA: Rungume-rungumen mu da Classiq tsautsayi ne - Rahama Sadau
Legit.ng ta samu cewa 'yan fim din dai sun yi ta yin sharhi game da lamarin ne a shafukan su na dandalin sada zumunta daban daban kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu.
T. Y. Shaba wanda ke zaman daya daga cikin wadan da suka yi tsokacin, ya zargi daya daga cikin jigogin masana'antar wanda ya taka rawar gani wajen ladabtar da Rahama Sadau a baya bisa fitowar ta a wani bidiyon waka inda take rungumar mawakin Classiq watau Nura Hussaini.
A wani labarin kuma, Shugaban hukumar nan ta tabbatar da da'a tare da dabbaka tarbiyya a jihar Kano ta Hisba watau Sheikh Malam Aminu Daurawa daga karshe ya yi tsokaci game da auren diyar Gwamnan jihar Fatima Abdullahi Ganduje da kuma angon ta Idris Ajimobi da ya gudana a jihar.
Bikin auren dai wanda ya gudana a ranar 3 ga watan Maris ya samu halartar manyan baki da dama daga sassa daban daban na kasar nan ciki kuwa hadda shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Sai dai jama'a da dama sun yi ta tsegumi game da yadda hukumar Hisba ta jihar ta yi gum game da yadda aka sheke aya a wajen bikin duk kuwa da haramcin hakan da hukumar ke nanatawa a cikin jihar.
Da yake tsokaci game da lamarin a shafin hukumar ta Hisba na Facebook, babban malamin ya bayyana cewa kwata kwata baya garin ne shiyasa.
A cewar sa, a ranar Asabar jim kadan bayan kammala dauren auren ne ya tafi jihar Sokoto domin halartar bikin kaddamar da littafin Mansur Sokoto daga nan kuma ya tafi jihar Zamfara kafin kuma ya wuce Kaduna inda anan ma yayi wa'azi sai a jiya ma ya dawo.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng