Kaico: Wani zaƙaƙurin ɗalibin jami’a ya hallaka kansa da kansa, ko me yayi zafi?
Hukumar gudanarwa ta jamia’r gwamnatin tarayya dake garin Bini na jihar Edo ta tabbatar da mutuwar wani zakakurin dalibinta da rahotanni suka tabbatar da ya kashe kansa da kansa.
Legit.ng ta ruwaito an tsinci gawar wannan dalibi mai suna Adams ne a dakinsa dake unguwar Ekosodin a karamar hukumar Ovia ta kudu na jihar Benuwe, inda aka bayyana dalibin a matsayin dalibin a ajin karshe a tsangayar ilimin kimiyyar kwamfuta.
KU KARANTA: Muhimmin darasi daga wata haduwa da aka yi tsakanin Sheikh Mahmud Gumi da wani Maroki
Daliban jami’ar UNIBEN sun bayyana Adams a matsayin hazikin dalibi mai sakamakon jarabawa na matakin mafi darajawa, wato First Class, inda suka kara da cewa ganin karshe da suka yi masa shi ne a ranar Alhamis inda ya mika wani aiki da aka basu bayan ya kammala.
Ganin kwanaki ba ji duriyar Adams ba, sai jama’a suka balla kofar dakinsa, inda suka tarar da gawarsa a rataye da silin din dakinsa.
Kaakakin hukumar UNIBEN Michael Osasuyi ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace “a lokacin da mahaifin yaron ya kai masa ziyara ne aka lura ba’a gansa ba a tsawon kwanaki, sai yan uwansa da abokai suka balla kofar, inda suka ganshi a rataye.”
Daga karshe, don kauce ma sake faruwar hakan a gaba, Kaakakin UNIBEN, Osasuyi ya bukaci daliban jami’ar da suk daure su dinga yin magana a duk lokacin da suke cikin wata matsala.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng