Gwamna Bello ya yi zazzaga, ya sauke dukkan masu mukaman siyasa a jihar Kogi

Gwamna Bello ya yi zazzaga, ya sauke dukkan masu mukaman siyasa a jihar Kogi

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya sauke dukkanin shugabannin kananan hukumomi 21 da kwamishinonin jihar.

Gwamnan da kansa ne ya bayar da sanarwar ana tsaka da gudanar da masu rike da mukaman siyasa a gidan gwamnati dake Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

Gwamna Bello ya yi zazaga, ya sauke dukkan masu mukamai a jihar
Gwamna Bello ya yi zazaga, ya sauke dukkan masu mukamai a jihar

KU KARANTA: Hotunan binne gawar tsohon gwamnan jihar Nasarawa

Wata majiya a fadar gwamnatin jihar ta shaidawa jaridar Premium Times cewar, gwamnan ya bukaci shugabannin kananan hukumomin da su mika makullan ofisoshinsu da motocin ga sakataren gwamnatin jihar.

Majiyar, da bata amince a ambaci sunanta ba saboda rashin samun izinin yin magana da manema labarai, ta ce, gwamna Bello zai sanar da wadanda zasu maye gurbin wadanda guguwar tayi gaba da su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng