Hotunan binne gawar tsohon gwamnan jihar Nasarawa
A yau ne aka binne gawar tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Aliyu Akwe Doma, a mahaifar sa, karamar hukumar Doma, jihar Nasarawa.
Tsohon gwamna Doma, ya mutu ne ranar Talata a wani asibitin kasar Isra'ila bayan wata gajeriyar rashin lafiya.
An kawo gawar sa Najeriya a jirgin Turkish a daren jiya Asabar da misalin karfe 11:00 na dare jiya.
Manyan 'yan siyasa, sarakuna da 'yan uwa da abokan arziki daga jihar Nasarawa da fadin Najeriya sun halarci jana'izar.
DUBA WANNAN: Ziyarar Buhari zuwa Benuwe: Jama'ar jihar sun gindaya masa wasu sharuda
Daga cikin manyan da su ka halarci jana'izar akwai gwamnan jihar, Tanko Almakura, tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Adamu, tsohon minista, Labaran Maku, tsofin mataimakan gwamnonin jihar da sauran su.
Aliyu Akwe Doma ya mulki jihar Nasarawa saga shekarar 2007 zuwa 2011.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng