Biki-bidiri da birede: Bayanai kan auren 'yar gidan Dangote da angonta
- A wata zantawa da manema labarai sukayi da Jamil ya bayyana masu abubuwa game da kansa da kuma aikinsa
- Za’ayi shagalin bikin a ranar 24 ga watan Maris, shekarar 2018, a jihar Legas
- Ana sa rai Tsofaffin shuwagannin Najeriya zasu harci bikin dama shuwagabannin wasu kasashen tare da Mashahurin mai kudi na Kimiyya, Bill Gate
Yanzu da aka fara shanin bikin anyi bikin ansa ranar shagalin Auren a ranar 17 ga watan Maris, shekarar 2018, wanda za’a daura auren a ranar 15 ga watan Maris, shekara ta 2018, a jihar Kano. Za’a karasa shagulgulan bikin a ranar 24 ga watan Maris, shekara ta 2018, a jihar Legas.
Ana sa rai cewa tsofaffin shuwagannin Najeriya biyar ne zasu halarci wannan biki tare da hamshakin mai kudinnan na duniya mai Kamfanin Microsoft, Bill Gate.
Ana ta yada labara a shafin labarai na yanar gizo-gizo game da yanda Fatima ke kama da mahaifinta, mashahurin Dankasuwar nan Aliko Dangote, kowa ya kalla ya san akwai kama a tsakani.
Jamil yana aiki da wani babban kamfanin Jirgin Sama a Najeria: An sanshi da sanya Agoguna masu tsada da kuma hawa manyan Motoci. 'Na fara ra’ayin tukin Jirgin Sama tun ina dan shakara 4. Ina son gudu. Tun ina karami ina son gudu, shiyasa nake hawan mashina masu karfi na gudu. Idan ka duba zakaga tabbuna a jikina duk da dai sun bacce ma yanxu, ina son tsere tun bay au ba nasha fadar haka'.
DUBA WANNAN: Za'a watse daga APC muddin...
Manyan ma’awaka na kasar na da suke abota kamar su Wande coal, Wizkid, Davido, K-Cee, Ice-Prince, M.I.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng