Gwamnonin APC biyu, na PDP uku da Sanatoci 35 zasu koma jam'iyyar SDP

Gwamnonin APC biyu, na PDP uku da Sanatoci 35 zasu koma jam'iyyar SDP

- Sakataren yada labaran jam'iyyar SDP, Mista Alfa Mohammed, ya ce jam'iyyar su zata kwace rinjaye a majalisar dattijai ta kasa kafin zaben 2019

- Ya ce wasu gwamnonin jam'iyyar APC biyu da na jam'iyyar PDP uku da kuma Sanatoci 35 sun kammala shirin komawa jam'iyyar SDP

- Ya bayyana jam'iyyar SDP a matsayin jam'iyya mai tsohon tarihi da ta ci zabuka a baya

Sakataren yada labaran jam'iyyar SDP na kasa, Mista Alfa Mohammed, ya bayyana cewar jam'iyyar su zata kwace rinjaye a majalisun tarayya kafin zaben 2019.

Mohammed ya ce a yanzu haka akwai wasu gwamnonin jam'iyyar APC biyu da na PDP uku da kuma Sanatoci 35 dake shirin komawa jam'iyyar SDP.

Mista Mohammed na wannan kalamai ne a wata hira da ya yi da wakilin jaridar Punch.

Ya ce jam'iyyar SDP ta fara jan hankalin 'yan siyasa ne saboda tsohon tarihin da jam'iyyar ke da shi musamman irin manyan zabukan da ta ci baya.

Gwamnonin APC biyu, na PDP uku da Sanatoci 35 zasu koma jam'iyyar SDP
Bashorun MKO Abiola lokacin yakin neman zabe a jam'iyyar SDP

Kazalika, Mohammed, ya kara da cewa rashin jagoranci nagari a manyan jam'iyyun Najeriya ya saka 'ya'yan jam'iyyun da 'yan Najeriya neman mafita domin fitar da Najeriya daga halin kangin matsin tattalin arziki da rashin tsaro da na aikin yi da ya dabaibaye ta.

DUBA WANNAN: Akwai jan aiki a gaban gwamnan Bindo na jihar Adamawa a 2019

Mohammed ya ce ba zai bayyana sunan sanatocin da gwamnonin ba amma ya ce sun fito daga kowanne bangare na kasar nan kamar yadda 'yan siyasa daga fadin Najeriya su ka hada karfi wuri guda wajen kirkirar jam'iyyar APC gabanin zaben 2019.

Ya kara da cewa, cin amanar 'yan siyasa da 'yan Najeriya da Jam'iyyar APC ta yi, ya saka su neman mafita a jam'iyyar SDP tare da bayar da tabbacin cewar jam'iyyar su ba zata sharewa 'yan Najeriya hawaye.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng