Matsalar muhalli ce ta haddasa rikicin manoma da makiyaya a Najeriya - Lai Mohammed
- Lai Mohammed ya ce bai bambancin addini da na kabilanci bane ya janyo rikici tsakanin manoma d makiyaya ba
- Matsalar muhalli ce ta haddasa rikicin manoma da makiyaya a Najeriya inji Lai Mohammed
Ministan watsa labaru da al’adu na Najeriya, Alhaji Lai Muhammad, ya ce matsalar muhalli ce ke janyo rikici tsakanin manoma da makiyaya a Najeriya ba matsalar bambancin addini ko na kabilanci ba kamar yadda ake zato.
Lai Mohammed ya bayyana haka ne a Birnin Berlin, a lokacin da yake ganawa da wasu wasu ‘yan Najeriya mazaunan kasar Jamus.
Minitsan ya kara da cewa, a shekarar 1963 yawan al’ummar Najeriya yana matakin mutane miliyan 48 kawai, amma a halin yanzu ‘yan kasar sun haura sama da miliyan 180 kuma kowa yana bukatar muhalli cikin harda filayen noma da kiwon dabbobi.
KU KARANTA : Fiye da 'yan sanda 2,000 aka tura jihar Filato saboda ziyarar da Buhari zai kai jihar
Mohammed ya ce samar wa miliyoyin 'yan Najeriya muhalli yana cikin kudirin gwamnatin shugaban kasa Muhammdu Buhari.
Masu sharhi sun ce idan ba a gagguta kawo karshen rikici tsakanin manoma da makiyaya ba da ya addabi wasu sassan kasar, al’amarin zai iya zama barazana ga zaman lafiyar kasar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng