Ji-ku-karu: Abubuwa 13 da ya kamata ku sani game da Nahiyarku ta Afirka

Ji-ku-karu: Abubuwa 13 da ya kamata ku sani game da Nahiyarku ta Afirka

- Afrika kyakkyawar nahiya ce mai Arziki da al’adu daban-daban wanda ya bambanta ta cikin nahiyoyi 7 na duniya

- Afrika nata albarkatu masu yawa, da kuma abubuwan sha’awa masu daukar hankali na shakatawa

- Afrika itace nahiya ta biyu a bangaren girma cikin nahiyoyin duniya kuma itace ta biyu a bangaren yawan mutane a nahiyoyin duniya

Abubuwa 13 da ya kamata ku sani game da Nahiyarku ta Afirka
Abubuwa 13 da ya kamata ku sani game da Nahiyarku ta Afirka

1. Afrika kwakkyawar nahiya ce mai Arziki da al’adu daban-daban wanda suka bambanta ta cikin cibiyoyi 7 na duniya.

2. Afrika na da albarkatu masu yawa, da kuma abubuwa masu daukar hankali na shakatawa. Zagaye da binciken nahiyar zai bayyana abubuwan sha’awa game da Afrika.

3. Afrika ta kasance itace nahiya ta biyu bangaren girma cikin nahiyoyin duniya, kuma itace ta biyu ta bangaren yawan mutane a nahiyoyin duniya.

4. Tana da fadin kilomita saqwaya miliyan 30.3 da tsawo na tsibirai, watau ta mamaye kashi 6 na fadin duniya. 5. Itace mai kashi 20 na yawan kasar duniya.

DUBA WANNAN: Wani Mulhidi a kasar Masar ya gamu da gamonsa

6. Afrika ta yaye ne daga hannun Turawan mulkin mallaka, banda kasar Itopiya (Habasha) da kasar Liberiya.

7. Afrika ce ta biyu na yawan mutane, inda take dauke da mutane a kalla Biliyan 1.1 ko ace kashi 16 na yawan mutanen duniya.

8. Ba'a fiye samun girgizar kasa a Nahiyar ba.

9. An wawashe jama'arta da arzikinta lokutan cinikin bayi da na mulkin mallaka. Kuma har yanzu arewacin nahiyar a hamadar Sahara yana hannun Larabawa ne.

10. Har yanzu nahiyar ita ce ta karshe wajen ci gaba da aiki da kwakwalwa.

11. Yakin duniiya na daya da na biyu bai shaffe ta sosai ba.

12. A nan ne aka fi ganin tsoffin kasusuwan dan-Adam, wanda hakan ya nuna a nan ne mutane suka fara bulla.

13. Da yawan kasashen dattijai da tun mulkin mallaka suke gwamnati, su da iyalansu ke mulki a nahiyar, musamman mulkin kama-karya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel