Wani Mulhidi ya gamu da gamonsa a kasar Misra, an kore shi daga gidan talabijin yana tsaka da hira

Wani Mulhidi ya gamu da gamonsa a kasar Misra, an kore shi daga gidan talabijin yana tsaka da hira

- Kasar Masar na kan tsarin sakulanci ne, amma addinin Islama aka fi bi

- Ana kara samu yawa-yawan samari da ke barin addininsu rana-tsaka a kasar

- An kore shi daga tsaka da hira sannan aka bukace shi ya je asibiti ya nemi lafiyar kwakwalwa

Wani Mulhidi ya gamu da gamonsa a kasar Misra, an kore shi daga gidan talabijin yana tsaka da hira
Wani Mulhidi ya gamu da gamonsa a kasar Misra, an kore shi daga gidan talabijin yana tsaka da hira

Wani saurayi a kasar Masar a makon nan, ya gamu da gamonsa, inda ana tsaka da hira dashi a gidan talabijin yace shi bai yarda akwai Allah ba, lamari da ya rikita hirar tasu wadda akwai wani babban Alaramma a ciki.

Mai gabatar da shirin dai, ya katse shirin gadan-gadan, inda yace bai taba jin shirme da sabo kaba'iri irin wannan ba. Bayan nan sai ma yace wa saurayin yana bashi shawara da yaje asibiti domin a duba kwakwalwarsa ko yana da tabin hankali.

Kasar Misra dai tana karkashin Islama ne tun bayan Amru bin Al-As ya ci Iskandariyya da yaki, shekaru 1350 da suka wuce, lokacin mulkin Sayyadi Ummaru, sai dai ana kara samun samari masu bijirewa tsarin Islama suna zama Mulhidai.

DUBA WANNAN: Abubuwa 7 da baku sani ba game da Yemi Osinbajo

Su dai Mulhidai sune wadanda basu bin kowanne addini, sun gwammace su bi tunaninsu, ko na wasu hamshaqan masu kwakwalwa, ko ma ilimin kimiyya na zamani. Wasunsu kuma suna komawa addinai da basu da abin bauta ne, kamar Buddhism.

Ko a Najeriya ana yawan samun irin wadannan samari da 'yan mata, sai dai ba safai sukan fadi hakan a bainar Jama'a ba saboda tsoron kulafucin idon masu bin addinai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng