Tiryan-Tiryan: Yadda aka kashe Buharin daji - kasurgumin barawon da ya addabi jihar Zamfara da kewaye
Mahukunta da jami'an tsaron jihar Zamfara dake a siyyar arewa maso yammacin kasar nan sun tabbatar da kashe kasurgumin barawon shanun nan mai suna Buharin Daji dake zaman jagoran barayin shanu da suka addabi jihar da kewayen ta.
Mun samu dai cewa wani babban jami'in gwamnatin jihar ya shaidawa majiyar mu cewa jami'an tsaro sun mika wa mahukunta gawar madugun 'yan fashin.
KU KARANTA: Sayar da jirage: Buhari ya kasa cika alkawarin sa
Legit.ng dai ta samu cewa cewa ranar Laraba da ta gabata ne aka kashe barawon shanun a wani farmaki da aka kai masa da taimakon wasu abokan fashinsa da suka raba gari.
Kamar dai yadda muka samu, sun raba gari ne da wani babban yaron sa mai suna Dogo Gide bayan da shi Buhari Tsoho din ya sa aka sato shanun surikin sa lamarin da bai yi masa dadi ba.
Mun samu cewa wannan ne ma ya sanya suka samu sabanin da yayi sanadiyyar kisan da aka yi masa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng