Ruwan Teku ya koro wata jaka dauke da hannayen mutane 54 a kasar Rasha

Ruwan Teku ya koro wata jaka dauke da hannayen mutane 54 a kasar Rasha

A ranar Juma'ar da ta gabata ne muka samu rahoton cewa, Teku ya wanko wata Jaka dauke da hannaye 54 na mutane a kasar Rasha daura da birnin Khabarovsk na Gabashin garin Siberia da yake iyaka da kasar Sin.

An tsinci wannan hannaye 54 cikin jakar in banda kwara guda da yake warea wani tsibirin kankara na gabar Tafkin Amur dake iyaka da kasar Rasha da kuma kasar Sin.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, masu sana'ar su a gabar ne suka tsinci wannan hannaye ne bayan sun ankare da jakar a yayin da suke bakin aikin su.

Hannayen kenan a gabar Teku
Hannayen kenan a gabar Teku

Har ila yau dai ba bu wani bincike da ya bayyana mamallakin wannan jaka ko kuma yadda aka saro hannayen kamar yadda jaridar Siberian Times ta bayyana.

KARANTA KUMA: Yadda wani Bawan Allah ya shafe shekaru 37 bai rasa Sallah a Masallacin Annabi ba

Hasashen mutane ya bayyana cewa, anyi amfani da gatari ne wajen sare hannayen daga gangar jikin su, yayin da wasu ke hangen an datso ne daga gawarwakin mutane dake killace a wani asibiti guda.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, sunan Allah ya bayyana jikin wata itaciya a yankin Ikorodu na jihar Legas.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng