Gwamnan jihar Neja ya sha da kyar a hannun wasu fusatattun matasa da suka masa rubuti da duwatsu

Gwamnan jihar Neja ya sha da kyar a hannun wasu fusatattun matasa da suka masa rubuti da duwatsu

Jama’a sun yi ma gwamnan Gwamnan jihar Neja atile da duwatsu a garin Bida, inda gwamnan ya kai ziyarar jajantawa ga yan kasuwan garin da Ibtilain gobara ya rutsa dasu wanda ya janyo musu asara mummuna.

Daily Nigerian ta ruwaito har sai da dogaran gwamnan suka dinga harbin iska don fafattakar matasan a lokacin da suke ihun ‘Sau daya’, ma’ana zangon mulki daya gwamnan zai yi, ko kuma ace babu tazarce.

KU KARANTA: Daga jin Mijinta zai kara aure, Matarsa ta banka ma gidansa wuta a Kebbi

Da aka tuntubi Kaakakin gwamnan, Jibrin Ndace, ya tabbatar da anyi jefe jefe, amma yace bashi da tabbacin ko gwamnan aka jifa ko kuwa a’a, saboda ba gwamnan bane kadai ya kai ziyarar, ya samu rakiyar manyan yan siyasan jihar da dama.

Ga bidiyon nan

Jibrin yace: “Daga cikin wadanda suka take ma gwamnan baya akwai: Sanata Mustapha Sani, Kaakain majalisar jihar Ahmed Marafa, shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Mikail Al0-Amin Bmitosahi, shugaban ma’aikatan jihar Sule Yabagi, kwmaishinoni, mashawarta, shuwagabannin APC da sauransu.

“Bayan ziyarar gani da ido da ya kai kasuwar, gwamnan ya tsaya a fadar mai martabar Sarkin Bidda, inda ya sanar da baiwa yan kasuwan tallafin naira miliyan 20, don haka nasan da ace akwai wani barazana ga gwamnan, tabbas da ya fice daga garin Bidda cikin gaggawa.” Inji shi.

Gwamnan jihar Neja ya sha da kyar a hannun wasu fusatattun matasa da suka masa rubuti da duwatsu
Motar Gwamna

A ranar Alhamis 8 ga watan Maris ne dai gobara ta lakume sama da shaguna 600 a tsohuwar kasuwa garin Bidda, inda majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnan jihar Yahaya Bello ya basu tallafin kui naira miliyan 20 don rage asara.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng