Saudiyya za ta ginawa 'yan gudun hijira na Syria masallatai 200 a kasar Jamus

Saudiyya za ta ginawa 'yan gudun hijira na Syria masallatai 200 a kasar Jamus

Masauratar kasar Saudiya ta dauki nauyin gina masallatai 200 a kasar Jamus, a sakamakon adadin 'yan gudun hijra na kasar Syria dake ta hauhawa wajen neman mafaka a kasar.

Ana ci gaba da suka tare da kalubalantar wasu kasashen larabawa masu arziki dake makwabtaka da kasar Syria, sakamakon rashin tallafa mata dangane da matsalolin jin kai da take fama da shi.

Wadannan kasashe da duniya ke kalubalanta sun hadar da; Qatar, Oman, UAE, Bahrain, Kuwait da kuma Saudiyya.

Saudiyya za ta ginawa 'yan gudun hijira na Syria masallatai 200 a kasar Jamus
Saudiyya za ta ginawa 'yan gudun hijira na Syria masallatai 200 a kasar Jamus

Da sanadin wata jaridar kasar Lebanon mai sunan Al Diyar mun samu rahoton cewa, Saudiya na kokarin wanke wannan kashi da ake goga mata, inda za ta gina masallatai 200 da kowane daya zai dauki 'yan gudun hijira 100 na Syria a kasar ta Jamus.

KARANTA KUMA: Ababe 16 da ya kamata 'yan Najeriya su sani game da Osinbajo

Wasu adalan rahotanni sun bayyana cewa, kasashen da duniya ke kalubalanta sun yi tarayya wajen bayar da mafaka ga miliyoyan 'yan gudun hijra na Syria a yayin da rikicin ya huro kai tun a shekarar 2011.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, rashin samun kusantar iyali na tsawon shekaru 4 ya sanya kwazabar wani Fasto ya dankarawa wata mata ciki a jihar Legas.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng