Ekwerenmadu zai fuskanci kuliya akan kadarorin da ya boye a kasashen waje
- Matsalar satar dukiyar kasa a kai kasashen waje ba abu bane sabo a kasar nan
- Gwamnatin Najeriya ta bi hanyoyi da dama ta karbe kadarori da yawa daga hannun manyan kasar nan amma kullum idan aka bincika sai an samo sabo
- A satin nan ne gwamnatin tarayya ta bankado kadarori da suke da alaka da mataimakin shugaban majalisar dattawa, wanda suke a kasar Ingila, Amurka da kuma kasar Dubai
Za’a gurfanar da mataimakin Shugaban majalisar Dattijai, Ike Ekweremadu, a gaban kotun shari’a ta aikata manyan laifuffuka (CCT), a mako mai zuwa, sanarwar ta fito daga ofishin ministan shari'a na tarayya.
Zai gurfana bisa laifin karya game da dukiyar daya mallaka, tuhumar dai daya yace da wadda ake yiwa Shugaban Majalisar Dattijai, Bukola Saraki, wadda kotu ta daga karar a ranar Alhamis dinnan.
DUBA WANNAN: Cutar mura mai karfi wacce zata iya sanadiyyar mutum milyan 300 su rasa ransu ta bulla a duniya
Ana dai zargin mataimakin shugaban majalisar dattijan da boye wasu kadarori a kasashen Ingila, Amurka da kuma kasar Dubai, wanda yaki ya bayyana su a gaban kotu a lokacin da jami'an gwamnati suke bayyana kadarorin su.
Ana saran jami'an hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), zasu bar kasar nan ranar Litinin zuwa kasar Dubai domin karbar kadarorin da aka alakanta su da Ekweremadu. Za a karbi kadarorin ne a bisa yarjejeniyar da ke tsakanin Najeriya da kasar Dubai, Wadda aka yi akan zata ke dawowa da Najeriya da duk wasu kadarori da suke da alaka da jami'an gwamnatin Najeriya.
Mista Ekweremadu, Sanata ne a jam’iyyar PDP tun shekarar 2003, an zabeshi a matsayin mataimakin shugaban majalissar dattijai a shekarar 2015. Inda aka zabi Sanata Bukola Saraki a matsayin shugaban Majalissar dattijai.
An yi hasashen cewa idan har an tabbatar da aikata laifinsu, to akwai kokwanton dukansu zasu iya rasa mukamansu kuma za’a a iya hanasu rike wani mukami na gwamnati har na tsawon shekaru 10.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng