Yadda wani Bawan Allah ya shafe shekaru 37 bai rasa Sallah a Masallacin Annabi ba

Yadda wani Bawan Allah ya shafe shekaru 37 bai rasa Sallah a Masallacin Annabi ba

A yayin da musulmai ke fafutikar neman tsira a gobe kiyama, su kan bi duk wani tafarki na jagoracin Annabi Muhammadu, Tsira da Aminci su kara tabbata a gare shi da iyalan sa, ta yadda ya tafi da al'amurran rayuwar sa da dabi'u wajen mu'amalantar al'umma.

Musulmai tun kafin wani lokaci da tunani zai iya kaiwa gare shi, suke iyaka bakin kokarin su wajen koyi da mafi tsarkakakken bawa.

A yayin haka ne wasu musulmai masu karfin imani ke fafutikar kiyaye duk wani tafarki da bin turba ta Manzon Tsira tare da kwadaitar da sauran 'yan uwasu romon da zasu tarar a gobe Kiyama.

Masallacin Fiyayyen halitta dake birnin Madina
Masallacin Fiyayyen halitta dake birnin Madina

Legit.ng ta samu labarin wani Bawan Allah da ya shafe shekaru 37 bai rasa Sallar jami'i ko sau guda a masallacin Fiyayyen Halittu dake birnin Madinah.

Haji Muhammad mutumin kasar Afghanistan ne da halin rayuwa na cirani ya hankado sa birnin Madinah tun yana saurayi dan shekaru 19 a duniya.

KARANTA KUMA: Dabdalar Rashawa: Mujallar Forbes ta cire attajiran Saudiya daga jeranton masu kudi na duniya

Tun daga wannan lokaci shekaru 37 da suka gabata, wannan bawan Allah yake rafka salloli a masallaci mai Alfarma kawowa yanzu.

Da yawan musulmai mahajjata da masu zuwa Umrah a kowace shekara zasu ga alamar sanayya a fuskar wannan Bawan Allah sanye da bakin rawani da kuma baki gemu dogo, sakamakon kasancewa a sahun gaba yayin kowace sallah a masallacin.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, mujallar Forbes ta cire attajiran kasar Saudiyya daga jeranton masu kudi na duniya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel