Da dumi-dumi: Mota dauke da man fetur ya kama da wuta

Da dumi-dumi: Mota dauke da man fetur ya kama da wuta

Wani mota dauke da jarkunan man fetur ya kama da wuta da safiyan nan a Allen Junction, Ikeja, jihar Legas.

Duk da cewa motan yak one kurmus, babu ran da aka rasa a wannan hadari.

Game da cewar idon shaida, daya daga cikin jarkunan da ke cikin motan ne ya fara tsiyayewa kuma ya sabbaba wannan wuta.

Wani ma’aikacin hukumar bada agaji na gaggawa a jihar Legas wanda aka sakaye sunansa yace, “Lokacin da wutan ya fara ci, mun samu labarin cewa yoyon man fetur ne ya sabbaba.”

Da dumi-dumi: Mota dauke da man fetur ya kama da wuta
Da dumi-dumi: Mota dauke da man fetur ya kama da wuta

Lokacin da wutan ya fara ci, mutane suka fito da gwangwani kasha wutansu amma mota ta tashi, kawai sai suka gudu domin neman tsira.

“Babu wanda ya matsa kusa da motan. Lokacin jami’an kasha wuta suka zo, sunyi iyakan kokarinsu wajen kasha wutan.

“Dukkan jami’an tsaro sun hallara domin tabbatar da cewa wannan abu bai gagara ba,” .

KU KARANTA: Ba na kulla wani kaidi kan Saraki…

Wani idon shaida yace lokacin da wutan ya fara, yan daban unguwan sun farwa yan sandan da ke wajen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng