Ba na kulla wani kaidi kan Saraki… tamkar ‘da yake gareni
Sanata Abdullahi Adamu mai wakiltan mazabar Nasarawa ta yamma y ace shugaban majalisan dattawa, Bukola Saraki, tamdar ‘da yake garesa kuma ba zai yiwu ya fara shirya kaidin tsigesa ba.
A ranan Alhamis, Sanata mai wakiltar Ebonyi ta tsakiya, Obinna Ogba, ya tuhumci Sanata Abdullahi Adamu na shirya wata kaidi na cire shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.
Mr. Ogba ya gabatar da hujjoji a yau Alhamis da ke nuna maganar wayan tarho tsakanin Sanata Adamu da wasu mutanen da suke shirin tare.
Amma sanata Abdullahi Adamu ya musanta wannan zargi kuma ya sabawa hankali wani yayi tunanin cewa yana kokarin cire shugaban majalisan dattawa.
Yace: “Wani abokin aikina ya kirani ya laburata min abinda ya wakana a filin majalisa a ayu. Abin ya bani mamaki kuma ya bata min rai,”
“Bana kokarin kada Saraki. Saraki tamkar ‘da yake gareni. Inada hakkin takaran kujeran shugaban majalisan dattawa shekaru 3 da suka wuce amma ban yi ba saboda ba so nike ba.”
“Saboda haka, ya sabawa hankali wani yayi tunanin inason kujeransa yanzu, wai kuma ina kokarin daburtawa majalisa lisafi. Ta wani dalili? Bai dace wani yayi irin wadannan maganganu ba.
“Mun kusa shekaru 3 a mulki yanzu, zabe ya matso kusa, kuma duk wanda yake tunanin cire shugabancin majalisa a yanzu na batawa kansa lokaci ne."
SHIN KA KARANTA WANNAN?: Dan majalisar tarayya ya bukaci Ministan Buhari ya ajiye mukamin sa
Adamu ya kalubalanci wadanda ke wannan zargin cewa su gabatar da hujjoji domin karfafa zargin da sukeyi.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng