Rashin samun kusantar iyali na tsawon shekaru 4 ya sanya na afkawa wata Matar - Inji wani Fasto
A ranar Alhamis din da ta gabata ne, wata Kotun al'adu ta Alagbado dake zamanta a garin Legas, ta gurfanar da wani Fasto dan shekaru 46 da laifin dankarawa wata mata ciki kuma ya amsa laifin sa ba tare da wata jayayya ba.
Faston dai ya bayyana cewa, ya aikata wannan aika-aika ne sakamakon rashin samun damar kusantar matar sa ta aure har na tsawon shekaru hudu.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, uwargidan wannan Fasto, Funmilayo, ta nemi Kotun ta raba tsohon auren dake tsakanin su na kimanin shekaru 16 sakamakon keta mata haddi da ya yi.
Rahotannin sun bayyana cewa, Funmilayo dai ta hana mijinta kusantar ta har na tsawon shekaru hudu da kwazaba irin ta da miji ta sanya ya gaza hakuri ya kauce hanya.
KARANTA KUMA: An damke wani Kare da laifin kisan Jaririya kwanaki 8 da haihuwar ta
A yayin zartar da hukunci, Alkalin Kotun Prince A.M Kosoko, ya umarci Aranse da biyan N15, 000 domin ci gaba da kulawa da 'ya'yen sa uku kafin Kotu ta kammala samun gamsassun hujjoji na yanke hukunci.
Alkali Kosoko ya dakatar da sauraron karar zuwa ranar 13 ga watan Maris domin ci gaba da shari'a.
Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Mujallar Forbes ta cire duk attajiran kasar Saudiyya daga jerin masu kudi na duniya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng