Manyan ayyukan raya kasa: Shugaba Buhari makiyin arewa ne - Buba Galadima
Tsohon masoyi kuma babban aminin shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari musamman ma a siyasance Injiniya Buba Galadima ya koka akan abun da ya kira yadda shugaban kasa yake yin shakulatin bangaro da yankin arewacin Najeriya musamman ma wajen aiwatar da ayyukan raya kasa.
Injiniya Buba Galadima ya bayyana takaicin sa akan cewa yadda shugaban kasar yayi sauri ya amince da kwangilar gina hanyar jirgin kasa mai tsawon kilomita 120 ta Legas zuwa Kalaba amma yayi burus da maganar gina tagwayen hanyoyin Kano zuwa Abuja.
KU KARANTA: Dakarun sojin Najeriya sun yi karin haske game da yiwuwar juyin mulki
Legit.ng ta samu cewa haka nan ma Inginiyan ya kuma bayyana cewa ko ma a kwangilar aikin hanyar jirgin kasa ta Kano zuwa Legas kamata yayi a fara yin hanyar daga dukkan bangaren amma sai aka faro ta daga Legas kawai.
A wani labarin kuma, Wasu gungun matasa 'yan jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress, APC da suka kira kansu masu ruwa da tsaki a jiya Alhamis sun bayyana karin wa'adin mulkin da aka yi wa shugaban jam'iyyar Cif John Odigie-Oyegun da mukarraban sa a matsayin abunda mai dace ba.
Matasan dai sun bayyana wannan matsayar ta su ne a yayin da suke wani taron manema labarai a garin Abuja jim kadan bayan kammala taron sirri da suka gudanar.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng