Musulmai za su mulki duniya, idan har suka rungumi Alkur'ani hannu biyu - Inji wani Fasto a kasar Rasha

Musulmai za su mulki duniya, idan har suka rungumi Alkur'ani hannu biyu - Inji wani Fasto a kasar Rasha

- A yanzu dai haka al'ummar musulmi ba irin ta'asar da basu aikatawa, saboda basu bin dokar abinda littafin su Alkur'ani mai girma ya ce

- Wani Fasto a kasar Rasha ya fito yana da'awar cewa addinin musulunci shine addinin gaskia. Amma ya ce musulmai ba za su taba ganin dai-dai ba har sai sun rungumi Alkur'ani hannu biyu

Musulmai za su mulki duniya, idan har suka rungumi Alkur'ani hannu biyu - Inji wani Fasto a kasar Rasha

Musulmai za su mulki duniya, idan har suka rungumi Alkur'ani hannu biyu - Inji wani Fasto a kasar Rasha

Wani babban fasto a kasar Rasha, Smirnov Dmitri Nikolaevich, ya bayyana cewa al'ummar musulmai za su sake rike mulkin duniya, amma sai sun rike Alkur'ani hannu biyu-biyu.

DUBA WANNAN: Asiri ya tonu: Gwamnatin Najeriya ta bankado wasu gidaje mallakar mataimakin shugaban majalisar dattijai a kasar Birtaniya, Amurka da Dubai

Bishop din ya bayyana hakan a lokacin da yake bayani a wani gidan talabijin dake kasar, inda ya ce:

"Duk wani mai son ya fuskanci Islama, ya rungumi Alkur'ani mai girma ba wai Musulmi ba. Alkur'ani tsaftacacce ne babu karya ko zalunci a cikin sa, inda musulman yanzu babu wani abu da ya bambanta mu da su. Ba abinda aka rubuta a littafin a Alkur'ani suke aikatawa ba, yanzu yaudara, karya, zalunci da duk wani aikin sabo Musulmai suna aikatawa. Sai dai nayi imani da wani abu: Na tabbata cewa makomar duniya tana a Musulunci. Musulmai za su mulki duniya, idan har suka rungumi Alkur'ani hannu biyu."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel