Zaben ƙananan hukumomi: Yan takarkaru 100 ke zawarcin kujerun Ciyaman 23 a jam’iyyar APC ta jihar Kaduna
Akalla yan takarkaru su 450 ne suka bayyana ma jam’iyyar APC reshen jihar Kaduna manufarsu ta darewa mukaman siyasa daban daban a zabukan kananan hukumomi dake karatowa.
Legit.ng ta ruwaito daga cikin yan takara 450, guda 100 na zawarcin kujerun shuwagabannin kananan hukumomi ne, yayin da 350 ke zawarcin mukaman kansilolin mazabu, kamar yadda mukaddashin sakataren jam’iyyar Yahaya Baba Pate ya bayyana.
KU KARANTA: Yan KAROTA sun ci na jaki a hannu direbobin A daidaita sahu a sakamakon wani hatsari da suka ja
Sakataren yace tun bayan sanar da siyar da fom na takara, yan siyasa ke ta kwararowa da nufin yankan nasu fom din don cikewa, wanda hakan ne zai tabbatar ma jam’iyyar shirin yan siyasan na tsayawa takara a zabukan dake karatowa.
Pate ya jaddada halascin jam’iyyar APC tsagin shugaban jam’iyya Shuaibu Idris Lauje, inda yace duk wanda ya siya Fom din takara a wajen wasu da ba su ba, yayi akin banza. “Kuna ganin dai yadda jama’a ke ta tururuwa don yankan Fom domin sun gamsu da jagorancin shugaban jam’iyya Shu’aibu Idris.
“A kullum adadin masu zuwa siyan Fom na karuwa, zuwa yanzu dai an samu mutane 350 da suka yanki fom din takarar kansila, da kuma 100 da suka yanki fom din takarar shuwagabannin kananan hukumomi 23 na jihar.” Inji Pate.
A nasa jawabin, Kwamishinan harkokin kananan hukumomi, Farfesa Kabir Mato ya yi watsi da tsagin APC na su Sanata Hunkuyi dake karkashin SI Danladi Wada, inda yace jam’iyyar APC na da ka’idoji da dokokinta na aiki, don haka babu wanda ya isa yayi ikirarin shugabancin jam’iyyar ba akan ka’ida ba.
Idan za’a tuna a baya dai rikicin jam’iyyar APC na jihar Kaduna ya dumama sosai, inda ta kai ga an kai ruwa an kai mari, har aka rushe sabon ofishin tsagin jam’iyyar dake hamayya da gwamnan jihar Malam Nasiru El-Rufai.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng