Nigerian news All categories All tags
Yayan majalisar dattawa sun yi tofin Allah tsine ga Gwamna Ganduje da Gwamna El-Rufai

Yayan majalisar dattawa sun yi tofin Allah tsine ga Gwamna Ganduje da Gwamna El-Rufai

Gwamnonin jihohin Kogi, Kano da Kaduna sun sha tofin Allah tsine daga wajen yayan majalisar dattawan Najeriya, wato Sanatoci a zaman majalisar ta ranar Alhamis 8 ga watan Maris.

Sanatocin sun zargi gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai da gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje da cin zarafin Sanatocin jihohin nasu don biyan bukatunsu, don haka suka yi tir da halayyar gwamnonin.

KU KARANTA: Wasu matasa sun yi ma wani Mahaukaci rubdugu a unguwar Fagge har sai da yace ga garinku

Sanatocin sun ikirarin gwamnoni a jihohi na shirya musu kitimurmura, inda suka ana ji ana gani aka haka Kwankwaso shiga jihar Kano, don haka muddin ba’a ci musu birki ba, hakan zai haifar da tarzomar da zata shafi zaben 2019, don ba zasu zura idanu ana ci musu zarafi ba.

Yayan majalisar dattawa sun yi tofin Allah tsine ga Gwamna Ganduje da Gwamna El-Rufai

Yayan majalisar dattawa

Sanatan Kogi ya tsakiya, Sanata Ahmed Ogembe ne ya fara nuna bacin ransa da yadda aka watsa wani taro da ya shirya da nufin tallafa ma jama’an mazabarsa da kayan dogaro da kai, tare da rusa gidajen magoya bayansa a garin Okene.

Shima a nasa jawabin, shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki ya nuna bacin ransa da abubuwa dake faruwa da Sanatoci a jihohinsu, yana cewa “Mun ga yadda gwamnan jihar Kaduna ya dau alwashin rusa gidan Sanata a jiharsa, kuma babu abinda muka iya yi.”

Da magana yayi magana, sai mataimakin shugaban majalisar, Ike Ekweremadu ya bayyana cewa idan aka cigaba da irin wannan, tabbas ba za’a tsira daga Sojoji ba idan suka shirya juyin mulki. Sai dai hakan bai yi ma jagoran marasa rinjaye a majalisar, Sanata Godswill Akpabio dadi ba, wada yace ba za’a kara ganin juyin mulki a Najeriya ba.

Daga karshe majalisar ta nada wani kwamiti da zai binciki korafin Sanata Ogembe, don tabbatar da gaskiyar lamarin, tare da bin diddigin rawar da rundunar Yansandan jihar ta taka a cikin bahallatsar, don daukan matakin daya dace.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel