Goron juma’a: Wani Fitaccen farfesa dan kasar Indiya ya karɓi Musulunci daga wajen Wazirin Sakkawato

Goron juma’a: Wani Fitaccen farfesa dan kasar Indiya ya karɓi Musulunci daga wajen Wazirin Sakkawato

- Farfesa Asokan na jam'iar jihar Sakkwato ya Muslunta

- Farfesan ya canza sunansa zuwa Muhammad Deen

Allah mai shiryar da wanda ya so, ya so wani fitaccen kuma hazikin Farfesa dan kasar Indiya da shiriya, wanda yake aikin koyarwa a jami’ar jihar Sakkwato, Farfesa Asokan, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Wannan Farfesa, kwararre ne a fannin ilimin kimiyyar Biochemistry, haka zalika shine shugaban kwamitin ladabtarwa na jam’ar jihar Sakkwato, kuma tsohon shugaban tsangayar kimiyyar Biochemistry.

KU KARANTA: Wasu matasa sun yi ma wani Mahaukaci rubdugu a unguwar Fagge har sai da yace ga garinku

Farfesa Asokan Chinnasamy ya nuna sha’awarsa ta shiga Musulunci, inda ya karbi shahada dag wazirin masarautar Sakkwato, Farfesa Sambo Wali, a yanzu haka Farfesa Asokan ya canza sunansa zuwa Farfesa Muhammad Deen.

Goron juma’a: Wani Fitaccen farfesa dan kasar Indiya ya karɓi Musulunci daga wajen Wazirin Sakkawato
Farfesa tare da Wazirin Sakkawato

Wanann cigaba da Farfesa ya samu ya faranta ma dayawa daga cikin daliban jami’ar rai, har ma da tsofaffin dalibai, wadanda suka ce Allah ne ya amshi addu’arsu, tunda dama sun dade suna yi masa addu’ar shiga Musulunci a sakamakon kyawawan halayensa, tausayi, mutunci da sanin ya kamata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng