Ababe 16 da ya kamata 'yan Najeriya su sani game da Osinbajo

Ababe 16 da ya kamata 'yan Najeriya su sani game da Osinbajo

A yayin da ranar haihuwa ta zagayo ga mataimakin shugaban kasa na Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, Legit.ng da sanadin jaridar Daily Trust tare da hadin gwiwa na Wikipedia ta kawo muku jerin ababe 16 da ya kamata 'yan Najeriya su ilmantu akai.

Farfesa Yemi Osinbajo

Farfesa Yemi Osinbajo

Ga jerin ababe 16 da ya kamata mu sani game da mataimakin shugaban kasar:

1. A yau ya cika shekaru 61 a duniya. An haife shi a ranar 8 ga watan Maris shekarar 1957 a jihar Legas.

2. Cikakken sunan mataimakin shugaban kasar shine, Oluyemi Oluleke Osinbajo.

3. Yana auren Dolapo Osinbajo, wadda jika ce ga tsohon shugaban Najeriya marigayi Obafemi Awolowo.

4. Osinbajo da Dolapo suna da 'ya'ya uku a tsakanin su.

5. Yayi karatun digiri na farko akan shari'a a jami'ar Legas a tsakanin shekarar 1975 zuwa 1978. ya kuma yi karatun digiri na biyu a fannin shari'a a jami'ar tattalin arziki ta birnin Landan a shekarar 1981.

6. Osinbajo ya fara karantarwa a jami'a tun yana shekaru 23 a duniya.

7. Tsohon lakcara ne na jami'o'i biyu dake jihar Legas.

8. Osinbajo shine babban mai bayar da shawara kan harkokin shari'a ga tsohon lauyan kolu kuma ministan shari'a na kasa, Bola Ajibola.

9. Shine lauyan kolu kuma kwamishinan shari'a na jihar Legas a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007.

10. Ya kasance shugaban limamai na cocin Olive Tree a jihar Legas kafin hawa kujerar mulki.

11. Mataimakin shugaban kasar yana daya daga cikin wadanda suka tsara manufofin jam'iyyar APC a yayin kafa ta tun a shekarar 2013.

KARANTA KUMA: An damke wani Kare da laifin kisan Jaririya kwanaki 8 da haihuwar ta

12. Ya kawo tsarin rarraba abinci kyauta da kuma allurar riga-kafi kyauta ga dalibai.

13. Osinbajo assumed office as the Vice President of Nigeria after taking the oath of office on 29 May 2015 at the Eagle Square, Abuja.

13. Ya karbi kujerar mataimakin shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2015.

14. Tsohon shugaban kasa Jonathan ya bashi lambar girma ta GCON (Grand Commander of the Order of the Niger) a ranar 28 ga watan Mayu na shekarar 2015.

15. Osinbajo shine mataimakin shugaban kasa na 14 a tarihin Najeriya.

16. Ya kasance mukaddashin shugaban kasa daga ranar 9 ga watan Mayu zuwa 19 ga watan Agusta na shekarar 2017.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel