Asiri ya tonu: Gwamnatin Najeriya ta bankado wasu gidaje mallakar mataimakin shugaban majalisar dattijai a kasar Birtaniya, Amurka da Dubai
- Gwamnatin Najeriya ta gano dukiya ta Miliyoyin kudi wadda keda ta alaka da Mataimakin Shugaban Majalissar Dattijai Mista Ike Ekweremadu a kasar Amurka, Birtaniya da Hadaddiyar Daular Larabawa wato Dubai
Gwamnatin Najeriya ta rubuta wa Hadaddiyar Daular Larabawa, kasar Birtaniya, da Amurka takarda, bayan ta gano wata boyayyun gidaje mallakar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai na Najeriya Mista Ike Ekweremadu, ya boye a kasashen.
DUBA WANNAN: An gano gonaki 5 da ake shuka tabar wiwi a garin Ringim dake jihar Jigawa
A cikin takardar da aka rubuta wa kasashen uku, Mr. Fowler na dogaro ne da yarjejeniyar kara ma juna sani, wurin bayyana dukiyar da aka boye a wata kasa wadda najeriya na da hannu a ciki. Yarjejeniyar wadda ta fara aiki a ranar 1 ga watan Janairu don kawar da mummunar hanyar dibar dukiyar al’umma.
Manufar wannan wasika shine don a sanar da mutanen kasa cewa gwamnati ta kawo ka’idar mallakar dukiya a kowace kasa ga ma’aikatan ta cikin kwanciyar hankali ba tare da fargaba ba, in ji Fowler.
A wasikar da aka rubuta wa Gwamnatin Amurka, zuwa ga cibiyar kula da harkokin mutane, a karkashin hukumar tsaro ta Amurka. An kuma aika da wata wasikar zuwa ga Tunde Fowler, shugaban hukumar karbar haraji na kasa.
A kasa hoton jerin kasashen da ya mallaki gidajen ne da kuma wuraren da suke.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng