Yadda jama'a suka tarbi shugaba Buhari a jihar Plateau cikin hotuna
- Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyara jihar Plateau a yau Alhamis
- Shugaban kasan ya kaddamar da wasu ayyuka da gwamnan jihar yayiwa al'ummarsa
Al'umman jihar Plateau sunyiwa shugaba Muhammadu Buhari laale marhabun da kawo ziyaran aiki jihar a yau Alhamis, 8 ga watan Maris, 2018.
Shugaba Buhari ya kai wannan ziyara ne domin kaddamar da wasu manyan ayyuka da gwamnan yayi a jihar. Kana zai gana da masu ruwa da tsaki a jihar domin ganin yadda za'a kawo karshen rikicin makiyaya da manoma da ke haddasa kashe-kashe a jihar.
Bayan sauka a filin jirgin saman Yakubu Gowon da ke garin Heipang, shugaba Buhari ya kai ziyara fadan Gbong Gwom Jos Da Jacob Gyang Buba tare da gwamnan jihar Simon Lalong; gwamnan jihar Nasarawa, Tanko AlMakura; ministan wasanni, Solomon Dalung; da sauran jami'an gwamnati.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng