Dabdalar Rashawa: Mujallar Forbes ta cire attajiran Saudiya daga jeranton masu kudi na duniya

Dabdalar Rashawa: Mujallar Forbes ta cire attajiran Saudiya daga jeranton masu kudi na duniya

A ranar Alhamis din da ta gabata ne, mujallar fitar da kowace kididdiga ta fadin duniya wato Forbes, ta bayyana cewa cire sunayen attajiran kasar Saudiya dage jerantaon masu kudi na duniya sakamakon dabdalar zargin na rashawa.

Mujallar ta bayyana cewa, ta cire sunayen hamshakan 'yan Kasuwa na kasar Saudiya mai arzikin man fetur a sakamakon gwamnatin kasar da take zargin su da aikata laifuka na rashawa tun a shekarar da ta gabata.

Da yawan attajiran sun shiga hannun hukumar wanda daga bisani aka sallamo bayan yarjejeniya ta makudan kudade da suka kulla da gwamnatin kasar.

Mujjalar ta Forbes dai ta bayyana cewa, ta cire sunayen attijarai 10 wadanda sunayen suka bayyana a kididdiga da jeranton masu kudin duniya a shekarar da ta gabata.

Yarima Alwaleed bin Talal
Yarima Alwaleed bin Talal

Yarima Alwaleed bin Talal, yana daya daga cikin attajiran da mujallar ta cire da jeranton da adadin dukiyar sa ta kai kimanin Dalar Amurka biliyan 18.7.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, akwai kuma Muhammad al-Amoudi da shi ma harkallar ta shafa wanda dukiyar sa ta kai kimanin Dala biliyan 8.1.

KARANTA KUMA: PDP ga Buhari: Ka yi koyi da shugaban kasar Ghana, ka daina kunyata Najeriya

Mujallar ta kara da cewa, adadin dukiya ta attajiran na Saudiya ta samu doriya akan Dala Biliyan 42.1 bisa ga adadin ta na shekarar da ta gabata.

Mujallar dai ta fitar da sunayen attajirai 2,208 a duniya da dukiyar su ta kai matakin Biliyan a shekarar nan ta 2018.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, akwai wasu sirrika 7 da ruwan Zam-Zam ya kunsa da ya kamaci kowane musulmi ya ribaci ilimin su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel