Nigerian news All categories All tags
Na yi iyakan kokarina – Buhari

Na yi iyakan kokarina – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce shi dai ya yi iyakan kokarinsa tun lokacin yah au karagar mulki a 2015.

A wata jawabin da mai Magana da yawunsa, Malam Garba Shehu ya saki ya bayyana hakan yau Alhamisa fadar shugaban kasa yayinda ya karbi bakuncin wani tawagar wakilan sarkin Salman na Saudiyya.

Shugaba Buhari y ace gwamnatinsa na sane da alkawura 3 da ta yiwa yan Najeriya kafin zaben 2015, yana bada tabbacin cewa ba zai yi kasa a guiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyin yan Najeriya.

Na yi iyakan kokarina – Buhari

Na yi iyakan kokarina – Buhari

“Tun lokacin da muka hau mulki zuwa yau, munyi iyakan kokarinmu, kuma zamu cigaba da mayar da hankali wajen cika alkawuranmu,” Cewan Buhari.

Ya kara da cewa yankunan da rikicin Boko Haram ne inda masu bada maki zasu gane irin canjin da aka samu tun lokacin da muka hau a 2015.

KU KARANTA: Kasar Birtaniya za gina gidan fursuna na fam 700,000 a Nigeria

Ya ce gwamnatinsa ta dukufa kan kare kasan nan, farfado da tattalin arziki da kuma dakile cin hanci da rashawa saboda yan Najeriya su fara amfana da arzikin kasan nan.

Ya mika godiyarsa ga cibiyar tallafi na Sarki Salman bias ga tallafin kudi 10 million dollars gay an sansanin IDP a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel