Yanzu-Yanzu: 'Yan shi'a sun tare hanyoyin garin Abuja, suna neman a saki Zakzaky

Yanzu-Yanzu: 'Yan shi'a sun tare hanyoyin garin Abuja, suna neman a saki Zakzaky

- Yan shi'a sun tare hanyoyin garin Abuja, suna neman a saki Zakzaky

- Hakan ya jawo cunkoson ababen hawa sosai inda hakan ne ma ya sanya wasu masu motoci canza hanya

Rahotannin da muke samu daga majiyoyin mu na nuni da cewa 'yan kungiyar nan ta 'yan uwa musulmi watau Islamic Movement of Nigeria, IMN a turance da aka fi sani da 'yan shi'a sun fita sun tattare wasu manyan hanyoyin garin Abuja suna zanga-zangar neman a sakar masu shugaba.

Yanzu-Yanzu: 'Yan shi'a sun tare hanyoyin garin Abuja, suna neman a saki Zakzaky
Yanzu-Yanzu: 'Yan shi'a sun tare hanyoyin garin Abuja, suna neman a saki Zakzaky

KU KARANTA: Iyayen yan matan Dapchi sun mamaye Abuja

Mun samu haka zalika cewa zanga-zangar ta su da suke cigaba da yi a saman manyan titunan babbar birnin kasar ta jawo cunkoson ababen hawa sosai inda hakan ne ma ya sanya wasu masu motoci canza hanya.

Legit.ng dai ta samu cewa a cikin masu zanga-zangar hadda mata, kananan yara da kuma matasa hadi da shugabannin 'yan shi'ar daga sassa daban daban na fadin kasar.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa gwamnatin ta tarayyar Najeriya karkashin shugabancin Muhammadu Buhari ce ke cigaba da tsare shugaban 'yan shi'ar Sheikh Ibrahim Zakzaky biyo bayan wata arangaba da mabiyan sa suka yi da jami'an tsaro a shekarar 2015.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel