Illolin ranto kudi daga China: Amurka ta gargadi Najeriya, kasashen Afrika

Illolin ranto kudi daga China: Amurka ta gargadi Najeriya, kasashen Afrika

- Sakataren harkokin waje na kasar Amurka, Rex Tillerson, ya gargadi kasashen Afrika a kan ranto kudi daga kasar China

- Ya yi kira ga kasashen da su yi duba na tsanaki kafin su amince da sharudan da kasar ta China ke gindayawa kafin bayar da rance

- Tillerson ya yi kaurin suna wajen sukar duk wata harka da ta shafi kasar China

Sakataren harkokin waje na kasar Amurka, Rex Tillerson, ya gargadi kasashen Afrika da su guji karbo rancen kudi daga kasar China.

Tillerson na wannan kira ne yau a kasar Ethiopia a rangadin da ya keyi na kasashen Afrika.

A cewar Tillerson, kasar Amurka ba adawa take yi da zuba hannayen jari da kasar China ke yi a kasashen Afrika ba ne, illa iyaka ta na gargadi ga kasashen Afrika din da su ke yin nazari da duba na tsanaki kafin amincewa da sharudan da kasar China ke sakawa kafin ta bayar da rancen kudi.

Illolin ranto kudi daga China: Amurka ta gargadi Najeriya, kasashen Afrika
Rex Tillerson

"Ba wai muna adawa da kasar China ko kashe kasuwar ta a kasashen Afrika ba ne, amma dole mu sanar da kasashen Afrika illolin dake tattare da karbar bashi daga kasar China," a cewar Tillerson.

Kazalika, Tillerson ya ce rancen kudi ba ya karawa kasa daraja musamman ta fuskar aiyukan raya kasa da samar da aikin yi.

DUBA WANNAN: Da duminsa: Jirgin yakin soji dauke da dakaru 32 ya yi hatsari, dukkan su sun mutu

"Babbar illar cin bashin kudin kasar China a wajen biya ne, domin zai yi wuya tattalin arzikin kasa bai durkushe ba ta hanyar mayar da kudin," inji Tillerson.

Idan baku manta ba, Legit.ng ta kawo maku rahoton cewar kasar China ta bawa Najeriya rancen kudi har dala biliyan $4.5 domin sayen kayan aikin noma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel