Abu namu: Manoman shinkafa 1,500 a garin Daura sun samu tallafi daga babban bankin Najeriya

Abu namu: Manoman shinkafa 1,500 a garin Daura sun samu tallafi daga babban bankin Najeriya

Akalla manoman shinkafa 1,500 ne suka samu tallafin kayan gona da babban bankin Najeriya CBN ke bayarwa a matsayin bashi, a karkashin shirinta na bunkasa harkar noman shinkafa da alkama a Najeriya.

Daily Nigerian ta ruwaito shugaban kungiyar manoman shinkafa, RIFAN, reshen garin Daura, Malam Nura Baure ne ya bayyana haka a yayin rabon kayayyakin a garin Daura a ranar Alhamis 8 ga watan Maris.

KU KARANTA: Kishi kumallon mata: Uwargida ta hallaka Mijinta da hanyar sheme shi da tabarya a jihar Neja

Majitar Legit.ng ta ruwaito Baure yana fadin duk manomin da yayi rajista da kungiyar RIFAN ya samu buhunan taki guda 2, kwalaben maganin feshi guda 2, buhunan iri guda 2, lita biyu na takin ruwa, buhu guda na takin kashin awaki da kuma injin ban ruwa.

Baure ya kiyasta darajar kayayyakin da manoman suka samu akan kudi N275,000, wanda ake sa ran kowanni manomi zai biya a cikin shekara daya, sai dai manomi zai biya kudaden ne a matsayin buhunan shinkafa ba kudin ake bukata ba.

Nura Baure ya gargadi manoma da su guji tserewa da kayan da nufin kin biya bashin, ko kuma siyarwa a kasuwa, inda ya tabbatar musu da cewa a yanzu haka akwai Kotunan da aka kafa don hukunta laifukan rashin biyan bashin ko na siyar da kayan aikin.

A nasa jawabin, shugaban RIFAN na jihar Katsina, Alhaji Shuaibu Wakili ya bayyana ma manoman cewa duk wanda ya biya bashin da aka bashi a cikin lokaci, za’a sake bashi wani bashin kayan aikin, ya kara da cewa ana sa ran manoma 18,000 zasu ci gajiyar wannan shiri.

Wannan shiri dai na samun tagomashin kudaden da manoman ke samu ne dag babban bankin Najeriya, CBN tare da bankin manoma da bankin inshora na manoma, duk da nufin samar da isashshen shinkafa a Najeriya, tare da tallafa ma manoma.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel