Rikicin majalisar dattawa: Sanata Abdullahi Adamu na shirya kaidin cire Bukola Saraki - Sanata Ogba

Rikicin majalisar dattawa: Sanata Abdullahi Adamu na shirya kaidin cire Bukola Saraki - Sanata Ogba

Sanata mai wakiltar Ebonyi ta tsakiya, Obinna Ogba, ya tuhumci Sanata Abdullahi Adamu na shirya wata kaidi na cire shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.

Mr. Ogba ya gabatar da hujjoji a yau Alhamis da ke nuna maganar wayan tarho tsakanin Sanata Adamu da wasu mutanen da suke shirin tare.

Sanatan yace: “Na mike da safen nan domin sanar da majalisa cewa akwai wani shiri da wasu keyi karkashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu. Zaku tuna cewa a watan Junairu, Sanata Misau ya yi wani magana cewa ana shirin cire shugaban majalisar dattawa da kuma shugabannin majalisa.”

Rikicin majalisar dattawa: Sanata Abdullahi Adamu na shirya kaidin cire Bukola Saraki - Sanata Ogba
Rikicin majalisar dattawa: Sanata Abdullahi Adamu na shirya kaidin cire Bukola Saraki - Sanata Ogba

“Yanzu ina da hujjoji cewa wasu suna shirin kawo rikita-rikita majalisar dattawa ta hanyan shirya zanga-zanga kuma an fara raba kudade. Dukkanmu shugabannin ne a wannan kasan kuma duk wanda ya ga abin da zai daburta lissafin kasa nan, majalisa ko demokradiyya, wajibi ya kawar da shi.”

“Ina son wannan majalisa a binciki wannan abu da kyau, inada hujjoji kan abubuwan da nike fada.”

KAYI KOKARI KA KARANTA: Ainihin dalilin da ya sa kotu ta bada belin Maryan Sanda

“Lokacin da Sanata Misau ya kawo wannan maganan a watan Junairu bamu daukeshi da gaske ba, wajibi ne mu tashi tsaye.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng