Shugaba Buhari ya isa jihar Plateau
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya isa filin jirgin saman Yakubu Gowon da ke garin Heipang jihar Flato misalin karfe 11:50 na safe.
Gwamnan jihar, Simon Lalong, tare da tsaffin gwamnonin jihar 2 kuma sanatoci a yanzu, Joshua Dariye da Jonah Jang; ministan wasanni, Solomon Dalung, tsohuwar mataimakiyar gwamnan jihar, Pauline Tallen da sauran su.
Ana sa ran shugaba Buhari zai kaddamar da wasu hanyoyi da gwamnan ya gina irinsu Mararaban Jama'a- Secretariat junction-British America junction road, Miango-Wild Life Park-Rafiki junction, Domkat Bali/Tudun Wada/old airport roundabout township roads da sauransu.
Kana kuma zai kaddamar da sabuwar shirin samar da zaman lafiya a jihar. Wannan shiri zai kwashe shekaru biyar domin aiwatar da shi.
KA KARANTA WANNAN KUWA?: Ka yi koyi da shugaban kasar Ghana, ka daina kunyata Najeriya
Zaku tuna cewa shugaba Buhari yayi alkawari zai kai ziyara dukkan jihohin da rikici ya shafa a kwanakin nan. A ranan Litinin, shugaban ya kai ziyara jihar Taraba inda ya gana da masu ruwa da tsaki a harkokin tsaron jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng