Mala’iku ne suka hana 'yansanda kama ni a Kotu – Dino Melaye

Mala’iku ne suka hana 'yansanda kama ni a Kotu – Dino Melaye

- Sanata Dino Melaye ya bayyana wa majalissar Dattawa yadda arcewa jami'an yansadan da suka zo kama shi a kotu

- Dino Melaye ya ce Mala’iku ne suka hana 'yansanda kama shi kotu

Dino Melaye,Sanata Mai wakiltar mazabar yammacin Kogi, ya bayyana wa majalissar Dattawa yadda ya arcewa zaratan rundunar ‘yansandar SARS da suka zo kama shi kotun Maitama.

Da yake yi wa majalissar Dattawa Jawabi, Sanata Dino Melaye yace yayi mamakin yadda jami’an ‘yansanda suka kewaye kotun domin kama shi.

“Ina cikin kotun aka fada mun cewa rundunar ‘yan sandan SARS su na jiran fitowa na daga cikin kotun dan su kama ni.

Mala’iku ne suka hana 'yansanda kama ni a Kotu – Dino Melaye
Mala’iku ne suka hana 'yansanda kama ni a Kotu – Dino Melaye

"Da na leko sai na gan su kusan 100. Kai ko cewa aka yi su je su kamo, Abubakar Shekau, iyakar shirin da za su yi kenan.

KU KARANTA : Rikicin kasuwan magani: Gwamnatin jihar Kaduna ta gurfanar da mutane 63 a kotu

"Ganin haka sai na ki fitowa, sai na fara yin adu’o’i dan samun mafita, daganan sai na fita daga kotu ba tare da sun san na fito ba, zan iya cewa mala’iku ne suka fice da ni, Don sai bayan ficewa na daga harban kotun da sa’o’i biyu suka son bana nan," Inji Melaye.

An maka, Sanata Dino Melaye, ne kotu a ranar 1 ga watan Maris, 2018, bisa zargin yiwa ‘yansanda karyar cewa shugaban ma’aikatan gwaman jihar Kogi, Edward Onoja ya tura mutane su kashe shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng