An gano gonaki 5 da ake shuka tabar wiwi a garin Ringim dake jihar Jigawa

An gano gonaki 5 da ake shuka tabar wiwi a garin Ringim dake jihar Jigawa

- Matsalar shan miyagun kwayoyi dai babbar matsala ce a kasar nan

- Gwamnati tana yin iya bakin kokarin ta wurin ganin ta hukunta duk wanda ta kama da laifin sha ko safarar kwayoyin, sai dai hakan bai saka ta canza zani ba, domin kuwa matsalar gaba take karawa ba baya ba.

- A yanzu haka an kama gonaki guda biyar a jihar Jigawa da ba su da aiki sai shuka tabar wiwi

An gano gonaki 5 da ake shuka tabar wiwi a garin Ringim dake jihar Jigawa
An gano gonaki 5 da ake shuka tabar wiwi a garin Ringim dake jihar Jigawa

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta (NDLEA) ta sanar da cewar ta binciko wasu gonaki guda biyar a karamar hukumar Ringim dake jihar Jigawa, wadanda ake shuka tabar wiwi.

Kakakin hukumar ta (NDLEA), Asguo Nkereumen, shi ne sanar da hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a wata sanarwa da ya fitar a Dutse babban birnin jihar a ranar Larabar nan. Ya bayyana cewa, sakamakon binciken da hukumar ta bada himma da yi a yankin, binciken ya sanya ta gano gonakin har guda biyar.

DUBA WANNAN: Amurka ta daina sayen danyen man fetur a Najeriya

"Hukumar ta gano gonakin ne a kauyukan Kagadama, Tsagan da kuma wasu kauyuka guda uku duka a yankin na Ringim din", a cewar kakakin rundunar.

Ya kara da cewa, masu shuka tabar wiwin sukan yi hikima ne ta hanyar cudanya ta da kayan lambu irin su Albasa, Tumatur da sauran su, domin kada a gane.

Kakakin hukumar ya ce, an kama daya daga cikin mutanen da ake zargi dauke da tabar wiwin da ta kai kimanin kilo 12.5, wanda ya yanko ta daga gona a ranar 26 ga watan Fabrairun wannan shekarar a kauyen Kagadama. A cewarsa, jami'an hukumar sun lalata daya daga cikin gonakin da take kauyen Tsagan, yayin da hukumar ke neman mai gonar ruwa a jallo.

Kakakin hukumar ya kara da cewar. gonaki ukun daga cikin gonakin suma an lalata su a lokacin da masu gonar suka ji labarin zuwan jami'an hukumar yankin. Ya ce wasu daga cikin mutanen yankin sun farwa jami'an hukumar, wanda sune suka taimakawa daya daga cikin masu gonakin ya gudu.

Ya kara da cewar, hukumar tana nan tana iya bakin kokarin ta domin ganin an kama masu laifin, sannan zata gurfanar da duk wanda ta kama a gaban kotu ba tare da bata lokaci ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng