Amurka ta daina sayen danyen man fetur a Najeriya

Amurka ta daina sayen danyen man fetur a Najeriya

- Abubuwa dai suna kara tabarbarewa a Najeriya, inda a yanzu haka kasar Amurka ta daina sayen danyen man fetur a kasar

- Daga shekarar 2000 zuwa 2006 kasar Amurka ita ce kasar da tafi kowacce kasa sayen danyen mai a Najeriya

- Amma tun daga shekarar 2015 bata kara saya ba

Amurka ta daina sayen danyen man fetur a Najeriya
Amurka ta daina sayen danyen man fetur a Najeriya
Asali: Depositphotos

Karamin Ministan Man Fetur na Najeriya, Dokta Ibe Kachikwu, ya ce Najeriya ta rasa cinikin dake tsakanin ta da kasar Amurka na danyen man fetur har abada, a matsayin ta na kasar da tafi kowacce siyan danyen mai a Najeriya.

DUBA WANNAN: Kasar Iceland tana kokarin saka dokar hana yi wa maza shayi

Ya ce har zuwa shekarar 2000, kasar Amurka ita ce kasar da tafi kowacce sayen danyen mai a Najeriya, inda take sayen kimanin ganga 700,000 a kowacce rana, inda a shekarar 2006 kuma ta kara sama daga ganga 700,000 zuwa ganga miliyan 1.31 a rana.

Ya ce tun daga lokacin ana ta samun raguwar sayen danyen man, inda kasar ta tsaya da sayen danyen man a shekarar 2015, bayan ta hada kai da kamfanin samar da mai na shale, inji Kachikwu.

Mista Kachikwu ya kara da cewa yanzu yankin Asiya sune suka fi son danyen man Najeriya din musamman ma kasar India. Ya ce yawan man da Najeriya ta ke fitar wa a kullum ya karu ya kai miliyan 2.07 a watan Fabrairun nan, kamar yadda ma'aikatar man fetur ta kasa ta kiyasta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel