Jam'iyyar APC bata da wani tsari na son kawo cigaba ga matasa - Dino Melaye

Jam'iyyar APC bata da wani tsari na son kawo cigaba ga matasa - Dino Melaye

- Majalisun kasar nan suna ta faman yunkuri na kafa hukumar tsaro ta Peace Corps

- Sanata Dino Melaye ya ce bashin da jam'iyyar APC ta ciyo a shekaru uku ya fi na shekaru sha shida da PDP taci yawa

- Sanatan ya ce zasu tirsasa shugaba Buhari ya saka hannu akan dokar ko yana so ko baya so

Jam'iyyar APC bata da wani tsari na son kawo cigaba ga matasa - Dino Melaye
Jam'iyyar APC bata da wani tsari na son kawo cigaba ga matasa - Dino Melaye

A ranar Talatar nan ne kafafen yada labarai suka dinga yada rahoton cewa Majalisar Dattijai da Majalisar Wakilai suna yin iya bakin kokarin su domin ganin sun tursasa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saka hannun akan dokar kafa hukumar tsaro ta Peace Corps.

DUBA WANNAN: Rikicin Siyasar Kano: APC zata iya korar Kwankwaso daga jam'iyyar bisa watsi da yayi da katin gayyatar bikin 'yar gidan Ganduje

Sanata mai wakiltar jihar Kogi, Sanata Dino Melaye, ya bada sanarwar a yayin da yake gabatar da kudurin majalisar, ya bayyana cewa, rashin nuna rashin amincewa da shugaban kasar yayi, hakan yana nuni da cewa jam'iyyar APC mai mulki bata da wani tsari na kawo cigaba ga matasan Najeriya.

Sanata Melaye ya kara da cewa yana samun matsin lamba daga mazabarsa akan dole gwamnati ta saka hannu akan hukumar Peace Corps din.

Sanatan ya kara da cewa a cikin shekara uku gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta aro kudin da yafi wanda jam'iyyar PDP ta ara a shekaru goma sha shida da ta yi tana mulki. A cewarsa a shekaru sha shiddan PDP ta ari kudi naira tiriliyan 6, yayin da ita kuma jam'iyyar APC mai mulki ta aro naira tiriliyan 11 a shekara uku.

Ya ce dole ne a sake duba yanda dokar Peace Corps din take, inda ya kara da cewa Majalisar Dattijai za ta tirsasa shugaban kasar ya saka hannu idan har ya nuna rashin yin hakan.

Sanatan ya ce "Ina son jawo hankalin majalisar dattijai akan batun Peace Corps. Mun karbi rahoto daga fadar shugaban kasa akan dalilin da yasa ba zai yarda ya saka hannu akan dokar ba. A yau na karbi sakonni da yawa daga mazabata inda suka yi imanin cewa Peace Corps abu ne wanda ya kamata shugaban kasa ya duba da idon basira.

"Hakan ta taba faruwa a lokacin da aka kirkiro hukumar tsaro ta Nigerian Security and Civil Defence Corps (NSCDC). A lokacin an gaya mana cewa babu kudi, yanzu gashi muna ganin amfani da aikin da suke yi a cikin al'umma.

"Muna so shugaban kasa yayi la'akari da matsayinsa, idan ba haka ba muna da karfin da zamu tirsasa shi dole ya saka hannu akan dokar.

Har aka gama zaman dai shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, wanda yake jagorantar zaman bai ce uffan ba, sannan kuma bai nuna alamun rashin goyon baya ba ga bayanin da Sanatan yayi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng