Tafiyayye ne: An karrama wani Malami dake shafe kilomita 42 a ƙasa a kullum don zuwa makaranta

Tafiyayye ne: An karrama wani Malami dake shafe kilomita 42 a ƙasa a kullum don zuwa makaranta

Wani jajirtaccen Malami dake shafe kilomita 42 a hanyarsa ta zuwa makarantar da yake koyarwa a kullum ya samu kyautar karramawa ta Fanka don a yaba masa tare da kara masa kaimi a aikinsa.

Malamin mai suna Auwudu Kombian yana koyarwa ne a makarantar Firamari dake Warvi D/A a kasar Ghana ya samu wannan kyauta ne a ranar fareti don bikin murnar cikar kasar Ghana shekaru 61 da samun yanci daga turawan mulkin mallaka, inji rahoton Yen.com.

KU KARANTA: Shari’a saɓanin hankali: Alkalin Kotu ya yanke ma wani ƙaramin Yaro hukuncin shara

Majiyar Legit.ng ta ruwaito baya da cin hanya a kullum, Kombia ne Malami guda taya tilo a makarantar dake da dalibai 74 da azuzuwa guda uku na tsawon shekara guda, kafin daga bisani a turo masa karin Malamai guda uku.

Tafiyayye ne: An karrama wani Malami dake shafe kilomita 42 a ƙasa a kullum don zuwa makaranta
Malamin

Wannan kyauta dai ta shiga hannun Kombian ne ta hannun daraktan ilimi na lardin, Ravaran Georgina Anaba Norga, wanda ya shawarci Malam Kombian y adage ya cigaba da kokarin da yake yi.

Da yake karbar kyautar Fankan, Malam Kombian yace: “Aikin da wuya, ba wani sauki, amma dayake aikina ne, kuma kwararren Malami ne ni, dole ta sanya nake iya bakin kokari na don shawo kan kalubalen. A kullum ina shafe tafiyar kilomita 42 zuwa makaranta, saboda babu dakin zama a makarantar ko a garin.” Inji shi

Daga karshe Kombian ya yaba da wannan karramawa da aka yi masa. “Ni ba ma ta Fankar nake ba, a’a. dadina shi ne da har aka lura da abinda nake yi, na ji dadi sosai.”

Sai dai wannan kyauta ta sha suka daga jama’a, musamman a shafukan sadarwar zamani, inda da dama daga cikin masu sukar suke ganin ba kyautar Fanka ya kamata a ba shi ba, kamata yayi a bashi kyautar Mota, ko Babur ko Keke.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng