Ya biya miliyan N1m domin a sace 'yar mutumin da nake bi bashin kudi
- An cafke wani malamin addinin Islama bayan samun shi da hannu cikin yunkurin sace diyar wani dan kasuwa dake zaune garin Legas
- Ya bayyana cewar ya biya wani mutum, Bagudu Bello, N100,000, somin tabi domin ya sace diyar dan kasuwar, Alhaji Salisu Idris
- Ya bayyana cewar dan kasuwar ya karbi miliyan N5m da niyyar zai taimaka ma sa ya sayi man fetur amma ya cinye kudin
An kama wani malamin Islama, Isah Idris, bayan samun sa da hannu cikin yunkurin sace diyar wani dan kasuwa mazaunin garin Legas, Alhaji Salisu Idris.
Idris ya biya wani mutum, Bagudu Bello, dake zaune a Kaduna somin tabin N100,000 domin ya sace diyar dan kasuwar saboda ya cinye masa kudi da yawansu ya kai miliyan N5m.
Idris ya ce dan kasuwar ya karbi miliyan N5m daga hannunsa da niyyar zai taimaka masa ya sayi man fetur amma har yanzu babu kudi babu fetur.
Kwamishinan 'yan sanda a jihar Legas, Imohimi Edgal, ya gabatar da Idris ga manema labarai a shelkwatar hukumar ta jihar Legas a jiya.
DUBA WANNAN: An raunata 'yan kasuwa 6 a harin da 'yan sara-suka su ka kai kasuwar 'yan canji
Edgal ya bayyana cewar Idris ne ya ambaci sunan Bello a matsayin mutumin da ya dauka haya domin ya zo Legas daga Kaduna ya sace diyar dan kasuwar.
Asirin su ya tonu ne bayan wanda aka dauko hayar ya sace yarinyar ya fahimci cewar mutumin da za a sace diyar sa sun fito ne daga gari daya kuma ya sha yi masa goma ta arziki a saboda haka ne ya yanke shawarar juyawa Idris baya.
Hukumar 'yan sanda ta ce zata gurfanar da su gaban kotu ba tare da wani bata lokaci ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng