An raunata 'yan kasuwa 6 a harin da 'yan sara-suka su ka kai kasuwar 'yan canji
- 'Yan kasuwar canji 6 ne su ka raunata sakamakon wani hari da batagari su ka kai kasuwar 'yan canji a Benin
- Batagarin sun kai harin ne a jiya tare da yin awon gaba da wasu kudaden kasashen ketare
- Wani shaidar gani da ido ya ce 'yan sara sukar sun yi kokarin kwatar kudi daga hannun 'yan kasuwar amma sai 'yan kasuwar su ka tirje
A kalla 'yan kasuwar canjin kudi 6 ne su ka samu raunuka bayan wasu batagari sun kai farmaki kasuwar hada-hadar kudade dake daf da kasuwar Ekiosa a birnin Benin na jihar Edo, a jiya.
Batagarin sun yi kokarin yin awon gaba da kudaden 'yan kasuwar, sai dai sun fuskanci tirjiya.
Afkuwar lamarin ta haifar da tsoro da fargabar ga mutanen dake harka a kasuwar.
Rahotanni sun bayyana cewar 'yan sara sukar sun yi nasarar tserewa da wasu kudaden kasashen ketare.
Wani shaidar gani da ido ya ce 'yan sara sukar sun kawo farmakin ne da niyyar diban kudi amma sai 'yan kasuwar su ka yi ta maza, su ka ki amincewa.
Daya daga cikin wadanda aka yi awon gaba da kudinsu, Muhammad Basiru, ya bayyana cewar daya daga cikin 'yan sara sukar ya kan zo shagon su ya roki kudi tare da bayyana mamakinsa bayan ganinsa ya gayyato abokansa domin su yi ma su sata.
DUBA WANNA: An samu ma'aikacin banki da hannu dumu-dumu cikin badakalar fiye da miliyan N700m
Shugaban Hausawa mazauna jihar Edo, Alhaji Gbadamasi Saliu, ya bayyana cewar yana ofishinsa lokacin da ya samu kiran cewar wasu batagari sun kaiwa Hausawa dake harkar canji farmaki.
Ya bayyana cewar har yanzu ba a kididdige adadin kudin da su ka dauka ba tare da bayyana jami'an tsaro sun kwantar da rikicin.
Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Chidi Nwanbuzor, ya ce babu wani sauran tarnaki yanzu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng