Bacewar mutane 21 a cikin ruwa: Ana zargin wani abu ne ya firgita yayin da su ke cikin kwale-kwale

Bacewar mutane 21 a cikin ruwa: Ana zargin wani abu ne ya firgita yayin da su ke cikin kwale-kwale

Kimanin mutane 21 'yan ci-rani dake kokarin tsallakawa zuwa kasar Cyprus ta Libiya ake nema har yanzu bayan an tsinci kwale-kwalen da ya dauko su babu kowa cikinsa.

A yanzu haka ana zargin ruwa ya cinye mutanen da ba a gani ba duk da babu wani sahihin rahoto a kan abinda ya faru.

Sashen kula da mutanen dake kaura zuwa kasashen ketare ya bayyana cewar wadanda su ka bace din na daga cikin mutanen dake yin bulaguro cikin yanayi mai matukar hatsari a cikin jiragen ruwa na katako da roba.

Bacewar mutane 21 a cikin ruwa: Ana zargin wani abu ne ya firgita yayin da su ke cikin kwale-kwale
Bacewar mutane 21 a cikin ruwa: Ana zargin wani abu ne ya firgita yayin da su ke cikin kwale-kwale

Wasu daga cikin wadanda su ka tsira sun ce wani abu ne ya firgita mutanen dake cikin daya daga cikin kwale-kwalen dake dauke da su.

DUBA WANNAN: Kwakwkwafi: Sanatan Najeriya ya bankado adadin tiriliyoyin da jam'iyyun APC da PDP kowacce ta ranto

Jami'an tsaro masu aiki a gabar tekun kasar Libiya sun kwashe wasu daga cikin wadanda ruwan bai cinye su ba zuwa kasar Libiya yayin da wani jirgin 'yan kasuwa na kasar Cyprus ya kwashi wasu ya zuwa garin Pozallo na kasar Italiya.

Kiyasin majalisar dinkin duniya ya ce kimanin mutane 421 ne su ka mutu a tekun bahar Rum cikin shekarar nan kadai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel